Ilimi Hasken Rayuwa
RFI Hausa
0
Wannan shirin yana fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a fannin ilimi a duniya, tare da nazari kan binciken kimiyya da fasaha da ke neman saukakawa dan'adam. Ana kuma jin ra'ayoyin masana kan yadda za a inganta rayuwar bil'adama. Shirin yana fitowa a duk ranar Talata da safe, kuma ana maimaita shi ranar Alhamis.
Epizode
-
Taron ƙaddamar da littafin tarihi na wani fitaccen matashi a Kanon Najeriya 30.06.2026 10minShirin na wannan mako ya mayar da hankali ne kan taron ƙaddamar da sabon littafin tarihin nan mai suna 'Mu San Magabata', wanda fitaccen matashin marubuci Kabiru Ahmad Kwalli ya rubuta da aka gudanar a jihar Kanon Najeriya. Taron ya haɗa masana, sarakuna, da ɗandazon al'umma domin duba yadda za a ceto tarihin ƙasar Hausa da ke shirin bacewa.
-
Yadda aka gudanar da taron manyan masana na duniya a birnin Lagos 23.06.2026 10minA wannan makon, shirin ya mayar da hankali ne kan babban taron ƙungiyar Lagos Studies Association karo na goma da aka kammala a ƙarshen mako, wanda ya saba haɗa masana, malaman jami'o'i, da masu bincike daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje domin tattauna halin da ilimi yake ciki a nahiyar Afirka cikin wannan ƙarni.
-
Yadda talauci ke hana ɗalibai cikar burinsu 09.06.2026 10minShirin Ilimi hasken rayuwa na wanna Mako ya mayar da hankali ne kan yadda matsin tattalin arziki ke tilstawa ɗalibai haƙura da cikar burinsu na karatu, don kawai neman abin kaiwa baka, a kowacce rana.
-
Shirin kawar da matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta na samun nasara a Jigawa 02.06.2026 10minShirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan makon ya sake waiwayar matsalar nan ce ta yawaitar yaran da ba za zuwa makaranta a arewacin Najeriya, batun da a fannin ilimi ke ci wa al’ummar yankin tuwo a ƙwarya.
-
Ɗimbin matasa na haƙura da karatun boko saboda rashin tabbas kan samun aiki 19.05.2026 10minShirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda matasa a baya-bayan na ke haƙura da ilimin boko saboda shakku kan yiwuwar samun aikin yi.
-
An yafe wa ɗaliban da ke son shiga kwalejin ilimi rubuta JAMB a Najeriya 12.05.2026 9minA yau muna ɗauke da wani labari mai daɗi ga ɗaliban da ke sha’awar zama malamai da kuma masu son shiga Kwalejin Ilimi a faɗin Najeriya.
-
Tasirin fasahar zamani wajen bunƙasuwar aikin jarida 05.05.2026 9minShirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan bikin ranar ƴancin ƴan Jaridu ta duniya da ke gudana a kowacce ranar 3 ga watan Mayu, bikin da ke zuwa a wannan karon cikin wani yanayi da aikin na Jarida ke ganin koma baya.
-
Yadda makarantun tsangaya suka fara gauraya karatun addini da na Boko don tafiya da zamani 28.04.2026 9minShirin Ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda makarantun tsangaya da na Islamiyya suka fara gauraya karatun addini da na zamani a ƙoƙarin da suke yi na tafiya da zamani da kuma amun tallafi daga gwamnatoci da manyan ƙungiyoyi na duniya.
-
Yadda mata a arewacin Najeriya ke yaƙi da jahilci don tallafawa ilimin ƴaƴansu - kashi na 2 22.04.2026 10minShirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon ci gaba ne kan yadda wasu daga cikin iyaye mata ke fafutukar neman ilimi a Kano, duba da yadda a wasu makarantu ake tambayar matakin karatunsu kafin ɗaukar yaran su a matsayin ɗalibai. Mafi yawan iyaye lamarin baya musu daɗi, wasu na zargin ƙin ɗaukar yaran, sai dai hanzarin shine sanin irin kulawar da ya kamata makarantun su baiwa yaran ne yasa suke tambayar.
-
Yadda mata a arewacin Najeriya ke yaƙi da jahilci don tallafawa ilimin ƴaƴansu - kashi na 2 21.04.2026 10minShirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon ci gaba ne kan yadda wasu daga cikin iyaye mata ke fafutukar neman ilimi a Kano, duba da yadda a wasu makarantu ake tambayar matakin karatunsu kafin ɗaukar yaran su a matsayin ɗalibai. Mafi yawan iyaye lamarin baya musu daɗi, wasu na zargin ƙin ɗaukar yaran, sai dai hanzarin shine sanin irin kulawar da ya kamata makarantun su baiwa yaran ne yasa suke tambayar.
-
Yadda mata a arewacin Najeriya ke yaƙi da jahilci don tallafawa ilimin ƴaƴansu 14.04.2026 10minA arewacin Najeriya, shigar mata makarantun yaki da jahilci ya fara ne a matsayin wani yunkuri na inganta rayuwar iyali da kuma tarbiyyar yara, inda mata da dama sun fahimci cewa rashin ilimi na hana su taimaka wa yaransu wajen karatunsu na zamani da kuma kulawa da lafiyarsu.
-
Wani matashi ya yi nasarar ƙera jirgi marar matuƙi a jihar Kano 07.04.2026 10minShirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon, ya yi dubi ne kan yadda wani matashi a jihar Kanon Najeriya ya ja hankalin jama’a, bayan ƙirƙirar jirgi maras matuƙi, daidai lokacin da matasan wannan ƙasa ke faɗi tashin yadda za su samo masu ɗaukar nauyin ayyukan fasahar da suke son cimmawa.
-
Yadda wasannin na'ura kwamfita ke samun karɓuwa a tsakanin matasa 31.03.2026 9minShirimmu na ilimi hasken rayuwa na wannan mako yayi karin bayani akan wasannin na’ura kwamfuta masu kama da gaske da aka fi sani da virtual reality a turance.
-
Tasirin faɗowar wasu sinadarai daga sama a fagen kimiyya da fasaha 03.03.2026 9minShirin "Ilimi Hasken Rayuwa" na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya yada zango ne a Jamhuriyar Nijar inda abaya-bayan nan aka rika samun fadowar wasu abubuwa daga sararin samaniya, lamarin da ke ci gaba da faruwa a sassan a kasar.
-
Ra'ayoyi sun banbanta kan amfani da fasahar AI wajen yin tiyata 24.02.2026 10minShirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako a wannan makon, ya mayar da hankali kan binciken da ya gano cewa shigar fasahar AI cikin fannin tiyata na haifar da wasu matsaloli masu kama da barazana ga rayuwar ɗan adam, kan haka ne ma muka zanta da masana a fannin kimiyya da kuma ɓangaren lafiya, inda muka jiyo ra’ayoyin mutane game da yadda wasu ke yarda AI ya duba lafiyarsu har ta kai ga tiyata a wasu lokutan.
-
Yadda satar jarabawa ke taka rawa wajen kassara ingancin ilimi a Najeriya 17.02.2026 10minShirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda satar jarabawa ke ƙoƙarin zama ruwan dare a makarantun sassan Najeriya, matsalar da ke ci gaba da illa ga ingancin ilimi a dukkan makarantu na ƙasar.
-
Yadda masu larurar ji ke fama da ƙalubalen karatu a Najeriya 10.02.2026 9minShirin na wannan mako ya ba da hankali ne akan yadda masu fama da larurar ji ke fama da ƙalubalen karatu a wasu sassan Najeriya.
-
Ana fuskantar koma bayan koyan harshen larabci a arewacin Najeriya 03.02.2026 9minShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya mayar da hankali ne kan dalilan da suka haddasa rashin koyon ingantaccen larabci tsakanin daliban sakandare a arewacin Najeriya, sabanin lokutan baya. A shekarun baya, alkaluma sun nuna cewa kusan kaso hamsin na larabcin da Dalibai ke koya suna samun sa ne a makarantun boko ba lallai sun sun halarci makarantun Arabiya, al’amarin dake neman zama tarihi a wannan zamani.
-
Yadda satar jarabawa da cin hanci da rashawa ke kassara ɓangaren Ilimi a Kamaru 27.01.2026 9minShirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda wani bincike can a Jamhuriyyar Kamaru ya gano yadda satar Jarabawa da cin hanci da rashawa ke mummunan tasiri a ɓangare ilimin ƙasar.
-
Makomar karatu a yankin arewacin Najeriya cike da barazanar ƴanbindiga 20.01.2026 9minShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya mayar da hankali kan makomar karatun ɗalibai a makarantun Najeriya musamman yankin arewaci mai fama da matsalolin tsaro, dai dai lokacin da aka koma sabon zangon karatu Iyaye na cike da fargaba kan tsaro a makarantu.
Popularan u
Ovaj podcast se pojavljuje i u podcast listama ovih zemalja.