Tambaya da Amsa
RFI Hausa
0
Shirin na RFI Hausa ne da ke amsa tambayoyin da masu saurare suka aiko. Ana gabatar da shirin a karshen mako, inda ake tattauna batutuwan da suka shafi masu sauraro. Yana ba da damar masu saurare su nemi bayani kan abubuwan da suke so su fahimta.
Episoder
-
Shirin tambaya da amsa na wannan mako ci gaba ne kan illar cutar olsa 02.05.2026 18minA yau shirin tambaya da amsa zai fara ne da ci gaban bayanin da muka faro a makon da ya gabata akan cutar gyambon ciki. -
Shirin tambaya da amsa na wannan mako ya ɗora ne kan illar cutar gyambon ciki 25.04.2026 18minA yau shirin tambaya da amsa zai fara ne da ci gaban bayanin da muka faro a makon da ya gabata akan cutar gyambon ciki. -
Tambaya da Amsa: Tasirin tsibirin Kharg ga tattalin arziƙin Iran 18.04.2026 19minShirin Tambaya da Amsa tare da Nasiru Sani, bisa al'ada kan amsa dukkanin tambayoyin da masu sauraro kan aiko, kuma guda cikin tambayoyin da shirin ya amsa a yau shi ne tasirin tsibirin Kharg ga tattalin arziƙin Iran. -
Illolin da ke tattare da makami ko makamashin Nukiliya 11.04.2026 18minShirin 'Tambaya da Amsa' kamar yadda ya saba a kowane mako, ya tuntuɓi masana a kan wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraro suka aiko mana domin samun Ilimi a kan ƙarin bayanin da suke nema. -
Akwai dokar da ta bai wa Amurka damar hukunta shugaban wata ƙasa? 07.03.2026 21minShirin 'Tambaya da Amsa' shiri ne da ke zuwa muku da amsoshin wasu tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana, kuma a kowane mako yake zuwa muku a daidai wannan lokaci. A yau shirin tambaya da amsa zai fara ne da bayani akan ko akwai wata doka da ta baiwa shugaban Amurka Donald Trump ikon hukunta wani shugaban ƙasa a Duniya. -
Tarihin kafuwar Ƙungiyar Kare Hakkin Ɗan Adam ta Duniya 28.02.2026 19minA cikin shirin Tambaya da Amsa daga sashen hausa na RFI,a yau shirin ya mayar da hankali ne kan tarihin kafuwar Ƙungiyar Kare Hakkin Ɗan Adam ta Duniya ta Human Rights Watch, wanda ya samo asali daga ƙoƙarin sa-ido kan yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa, musamman a lokacin yaƙin cacar baka. -
Tasirin taron tattalin arziki na Davos da ya gudana a Switzerland 31.01.2026 19minA cikin shirin Tambaya da Amsa daga sashen hausa na RFI,a yau shirin zai dora ne a cigaban tattaunawa a kan tasirin taron Davos wadda aka saba shekara-shekara kan duba lamuran tattalin arzikin duniya. Ga ci gaban tattaunawa tare da Dr. Kasim Garba Kurfi masanin tattalin arziki na ƙasa da ƙasa dake tarayyar Najeriya. -
Menene yake haifar da sukar ciki ko kuma naɗewar hanji a cikin ɗan Adam 24.01.2026 21minShirin tambaya da amsa na wannan mako zai fara ne da bayani akan abinda ke haifar da sukar ciki ko kuma naɗewar hanji a cikin mutum. -
Me ya sa darajar kuɗaɗen wasu ƙasashen larabawa su ka fi na Amurka daraja? 17.01.2026 20minShirin tambaya da amsa da ke zuwa muku da wasu amsoshin tambayoyin da masu sauraronmu su ka aiko mana, mu kan mika wadanan tambayoyi ga masana domin baku amsar da ta dace................ -
Tambaya da amsa: Ko ta yaya ake gane ƙarfin tattalin arziƙin ƙasa? 10.01.2026 21minShirin Tambaya da amsa tare da Nasiru Sani a wannan makon ma bai yi ƙasa a gwiwa ba, inda ya amsa wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraro suka aiko mana kamar yadda aka saba. -
Ko shan magani na yiwa ɗan Adam illa ? 03.01.2026 21minA cikin shirin tambaya da amsa na wannan mako daga sashen hausa na Rfi,shin ko gaskiya ne duk magani da mutum ya sha ya na da tasa illar da zai masa? Nasiru Sani ya tunttubi masana a kai..... -
Tarihin kafuwar kungiyar SASSAKAWA foundation 20.12.2025 20minTarihin kafuwar kungiyar SASSAKAWA foundation dake taimakawa a harkar manoma a Najeriya, wai shin da gaske ne kungiyar daga Japan aka kafata kuma wanene ya kafata? Akan wannan tambaya ce muka zanta da Dr Abdulhamid Gambo mataimakin shugaban SASSAKAWA Foundation a Najeriya. -
Tambaya da Amsa: Taƙaitaccen tarihin Marigayi Sheikh Ɗahiru Bauchi 06.12.2025 20minShirin Tambaya da Amsa tare da Nasiru Sani, bisa al'ada kan amsa tambayoyin da masu sauraro suka aiko, inda a yau guda cikin tambayoyin da wannan shiri ya amsa shi ne buƙatar taƙaitacce tarihin fitaccen Malamin Islaman nan a Najeriya kuma jigo a Dariƙar Tijjaniya, shehu Usman Dahiru Bauchi wanda Allah ya yiwa rauswa a ranar 27 ga watan Nuwamban shekarar da muke ta 2025 . -
Tarihin shahararren jarumin fina-finan indiannan Dharmendra 29.11.2025 20minShirin tambaya da amsa na wannan mako ya mayar da hanakali ne a kan tarihin shahararren jarumin fina-finan indiannan wato Dharmendra wanda ya rasu a ranar 24 ga watan Nuwamban shekarar 2025. -
Abubuwan dake haddasa cutar toshewar hanyoyin numfashi wato Asthma 22.11.2025 20minShirin Tambaya da Amsa na wannan mako, zai fara ne da bayani dangane da abubuwan dake haddasa cutar toshewar hanyoyin shaƙar numfashi wato Asthma a turance. -
Abubuwan da ke haddasa warin baki da kuma hanyoyin magance matsalar 18.10.2025 19minShirin tambaya da amsa na wannan mako tare da Nasiru Sani, ya amsara tambaya akan abinda ke haddasa warin baki da kuma hanyoyin da ya kamata abi wajen magance matsalar. -
Ƙarin bayani akan adadin Nahiyoyin duniya da kuma wacce ce ta fi faɗin ƙasa 11.10.2025 19minShirin tambaya da amsa na wannan mako tare da Nasiru Sani, ya amsa tambayoyin da ke neman karin bayani akan inda tsakiyar Najeriya ya kasance, da tambayar da ke neman sanin Nahiyoyi nawa ne a duniya kuma wacce ce ta fi faɗin ƙasa sannan wacce ta fi yawan mutane? da kuma tambayar da ke cewa, don Allah ku tambaya mana masana tattalin arziki akan mece ce TIN number kuma ina ake samunta sannan mene ne aikinta a Najeriya? -
Cigaban bayani bayani akan kafa sabuwar rundunar sojin ko-ta-kwana ta ECOWAS 04.10.2025 20minA yau shirin tamabaya da amsa zai fara ne da cigaban amsar tambayar dake neman karin bayani akan sabuwar rundunar sijin ko-ta-kwana wadda ƙungiyar ECOWAS ke shirin kafawa, da kuma cigaban amsar tambayar da aka yi game da cutar daji mafitsara... Wanna da ma wasu tambayoyin ne za mu amsa a cikin shirin 'Tambaya Da Amsa na wannan makon. -
Ƙarin bayani akan kafa sabuwar rundunar sojin ko-ta-kwana ta ECOWAS 27.09.2025 19minA yau shirin tamabaya da amsa zai fara ne da tambayar dake neman karin bayani akan sabuwar rundunar sijin ko-ta-kwana wadda ƙungiyar ECOWAS ke shirin kafawa.. Wanna da ma wasu tambayoyin ne za mu amsa a cikin shirin 'Tambaya Da Amsa na wannan makon. -
Harajin kashi 5 da gwamnatin Najeriya ke son ƙarawa akan kuɗin man fetur 20.09.2025 21minKo menene harajin kashi 5 da gwamnatin Najeriya ke son ƙarawa akan kuɗin man fetur ga duk mai bukata?, Ku tambaya mana masana harkokin tsaro domin su yi mana bayani akan mene ne ma'anar ƴansandan jihohi da ake ta muhawara a kai a Najeriya, kuma shin yin hakan zai haifar da ɗa mai ido? wasu cikin tambayoyin masu sauraro kenan da shirin Tambaya da Amsa na wannan mako ke ɗauke da amsoshinsu tare da Nasiru Sani....
Populær i
Denne podcast optræder også i podcast-hitlister i disse lande.