Muhallinka Rayuwarka
RFI Hausa
0
Wannan shirin na RFI Hausa yana wayar da kan jama’a da kuma ilmantar da su game da harkokin noma, muhalli da canjin yanayi. Yana ba da bayanai kan gurbacewar yanayi da kuma dumamar duniya. Har ila yau, shirin yana taimaka wa masu sauraro su fahimci yadda za su kare muhallinsu. Ana kuma tattauna batutuwan da suka shafi rayuwar yau da kullum da ci gaban aikin gona.
Episodios
-
Ƙarancin yashin gini na haddasa rikici tsakanin jama'a da illa ga muhalli 15.08.2026 20mA wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan yadda aikin gine gine ke haddasa bukatar yashi wanda nemanshi ke zama matsala tsakanin jama'a, da kuma illa ga muhalli da wurin noma da hanyoyin ruwa da sauransu. -
Yadda dazuka ke taimakawa wajan kare muhalli 08.08.2026 20mShirin Muhallinka rayuwarka na wannnan mako tare da Nasiru Sani ya duba irin gudun mawar da ganzun daji ke bayarwa wajan kare muhalli daga matsalar sauyin yanayi -
Yadda dazuka ke taimakawa wajan kare muhalli 08.08.2026 20mShirin Muhallinka rayuwarka na wannan mako tare da Nasiru Sani ya duba irin gudun mawar da dazuka ke bayar wa wajan kare muhalli daga matsalar sauyin yanayi. -
Matakan da manoman Nijar ke ɗauka a lokutan da aka fuskanci ƙarancin ruwan sama 02.08.2026 19mA Jamhuriyar Nijar,manoman dai sun fara da taka tsan-tsan ne saboda tsila-tsillar saukar ruwan shukar da suke fuskanta da kuma yanda ake samun dogon lokaci kafin saukar wani ruwan bayan saukar na farko, abun dake sanya shukar da suka yi ta mutu a ɗan wani lokaci. -
Illolin karancin gonaki kusa da jama'a da yadda ya shafi burin bunkasa samar da abinci 25.07.2026 19mSau da dama, masu burin shiga harkokin noma a Nigeria kan canza tunaninsu, sakamakon rashin samun gonakin da za su noma kusa da gari, lamarin da kan tilasta su jingine aniyarsu ta yin noma. Gwamnatin Nigeria dai, ta sha kira ga ‘yan kasar da su koma gona, la’akari da yadda Allah ya albarkaci kasar da wadatattun filayen noma da kuma yanayi mai kyau da za a iya noma kowane irin nau’in kayan abinci. -
Matsalar ambaliyar ruwa da kan dagula lamuran al’uma a Najeriya 20.06.2026 19mKamar kowace shekara, a bana ma ana hasashen samun ambaliyar ruwa a wasu ƙasashen yammacin Afrika, inda akan samu rasa rayuka da dukiya mai tarin yawa. A Najeriya, an sha samun hasarar rayuka a sanadin matsalar ambaliyar ruwan, da kan rutsa da wasu yankunan ƙasar. -
Masana na ci gaba da tsoratar da al'umma game da illolin da ke tattare da gurɓatacciyar iska 13.06.2026 19mA wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan tasirin gurɓatacciyar iska ga lafiyar halittu da muhalli wato air pollution a turance. Iska na gurɓa ta ne ta hanyoyi da dama, kama daga hayaƙin na’urori wato injina a masana'antu, zuwa tarkacen bola ko kuma ƙone wasu abubuwa, wanda su ke kawo cikas ga yanayin muhalli tare kuma da kawo tazgaro ga lafiyar ɗan Adam. -
Kananan manoma a Najeriya na nan kan tsarin noma na kaka da Kakanni 06.06.2026 19mA yau wannan shiri zai ba da hankali ne akan yadda har yanzu, kananan manoma a Nigeria na nan kan tsarin noma na Kaka da Kakanni, lamarin da ake gani yana hana ruwa gudu wajen tabbatar da cimma burin kasar na kasancewa mai dogaro da-kai a fannin samun wadatar abinci. -
Yawaitar takin jabu ya zamewa Manoman Najeriya ƙalubale a bana 23.05.2026 19mShirin 'Muhallinka Rayuwarka na wannan makon, ya tattauna ne da masu ruwa da tsaki kan sha'anin Noma, a kan matsalar yawaitar taki da kuma magungunan ƙwari na jabu, matsalar da ta zamewa manoman Najeriya ƙalubale babba a shekarar bana. -
Sauyin Yanayi ya jefa Manoma cikin ruɗani kan lokacin da ya dace su fara shuka 16.05.2026 18mShirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon ya tattauna na a kan yadda samun saukar Ruwan Sama na farko a bana ya jefa manoma a jihohin Arewacin Najeriya cikin ruɗani dangane da lokacin da ya dace su fara shuka. -
Yadda saukar ruwan sama na farko ya jefa manoma cikin ruɗani 09.05.2026 18mA yau wannan shiri zai ba da hankali ne akan yadda Ruwan sama na farko da aka samu a baya-bayan nan ya jefa manoma a jihohin Arewacin Najeriya cikin ruɗani da fargaba, yayin da hukumar hasashen yanayi ta ƙasa, NiMet, da masana ke gargaɗi game da tsagaitawar ruwan saman da wuri wanda zai iya lalata duk wani amfani da aka yi a wannan lokaci. -
Matsalar karancin tsaftataccen ruwa, na ci gaba da addabar iyalai a sassan Nigeria 02.05.2026 20mMatsalar nan ta karancin tsaftataccen ruwa, na ci gaba da addabar miliyoyin iyalai a sassan Nigeria, kila ko saboda rashin samun damar jan ruwan famfo a gidajensu, ko kuma rashin samun ruwan daga hukumomin samar da ruwan famfo na jihohinsu, duk da makudan kudin da gwamnatocin jihohin ke warewa, da sunan samar da ruwa wa jama’arsu. -
Karfafa gwiwa ga jama'a su koma noma a jamhuriyar Nijar 25.04.2026 20mShirin muhallinka rayuwarka na wannan mako zai maida hankali ne kan yanda ake karfafa gwiwa ga jama'a su koma noma don ita ce babbar hanyar dogaro da kai ta fuskar abinci. -
Matasan kasashe 11 da ke cikin tsarin shingen kare Hamada suka kai rangadi a Nijar 19.04.2026 18mA yau shirin zai leka jamhuriyar Nijar ne inda matasa daga kasashe 11 da ke cikin tsarin shingen kare Hamada da zaizayewar kasa don mayar da yankin tsanwa suka kai rangadi a Nijar musaman a Jihohi 5 na kasar da suka hada da Tillaberi Niamey, Dosso, Maradi da Zinder don duba irin cigaban da Nijar ta samu a wannan fannin da nufin kwaikwayonsa don kaddamar da shi a kasashensu. -
Dalilan da suka sanya Manoma Albasa a Nijar fuskantar ƙalubale a bana 14.04.2026 20mShirin 'Muhallinka Rayuwarka' na wannan makon, ya yi tattaki zuwa Jamhuriyar Nijar, inda aka fuskanci ƙalubale kan noman Albasa a shekarar bana. -
Yadda sare itace a Nijar ke haifar da koma baya wajen samun amfanin gona 04.04.2026 20mShirin, ‘Muhallinka Rayuwarka a wannan makon ya yi duba ne kan yadda ake samu canjin yanayi ta hanyar saran icen "Gawo" barkatai daga Makiyaya da su kansu Manoman, wanda ake ganin ke haifar da koma baya wajen samun yalawar abinci kamar, bakamar yadda aka saba ba a shekarun baya a cikin gonaki na Jamhuriyar Nijar. -
Hukumar NIMET ta yi hasashen samun saukar ruwa da wuri a daminar bana a Najeriya 14.03.2026 20mShirin ‘Muhalinka Rayuwarka’ a wannan makon ya yaɗa zango ne a Tarayyar Najeriya, inda ya mayar da hankali kan hasashen ruwan sama da Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya NIMET ta yi, gabanin kamawar daminar bana, inda ta bayyana cewa damina za ta sauka da wuri a jihohi irin su Kano da Niger da Rivers da wasu jihohi 12 na ƙasar. -
Yadda cutar tumatiri ta kasara manoma a wasu jihohin arewacin Najeriya 31.01.2026 20mShirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ tare da Michael Kuduson a wanan mako ya yi duba kan wata mummunar cutar tumatiri da ake kira Tuta Absoluta ko kuma cuta mai karya garkuwar tumatir. -
Dalilan da masana suka ce su ke ƙara bayyana sauyin yanayi 11.01.2026 20mShirin muhallinka rayuwarka na wannan makon ya tattauna ne kan yadda sauyin yanayi ko dai na zafi ko na sanyi ko kuma damina ke bayyana ƙarara, musamman a yankin yammacin Afirka. Ga misali a Najeriya, ɗaya daga cikin sauye-sauyen yanayin da aka shaida shi ne rashin hunturu a shekarar bana, musamman a Yankin arewacin ƙasar, inda aka saba ganin kankamar Yanayin na sanyin mai tsanani daga ƙarshen watan Nuwamba ko farkon Disamba zuwa ƙarshen watan Janairu ko farkon Fabarairu. -
Noman rani na fuskanta barazana a Najeriya sabida tsadar kayan noma irinsu taki 13.12.2025 20mShirin, ‘Muhallinka Rayuwarka’ a wannan makon ya yaɗa zango ne Tarayyar Najeriya, inda ya duba irin barazanar da noman rani ke fuskanta, musamman a wannan lokaci da farashin kayyakin gona suka faɗi warwas a yayin da farashin taki da sauran mahimman kayakin da ake amfaani da su wajen noman suke a can ƙololuwa.
Popular en
Este podcast también aparece en las listas de podcasts de estos países.