Lafiya Jari ce
RFI Hausa
0
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama'a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.
Jaksot
-
Ƙaruwar masu fama da cutar sikila a Jamhuriyar Kamaru 29.06.2026 10minA wannan makon shirin ya yi duba ne kan ƙaruwar masu fama da cutar sikila a jamhuriyyar Kamaru bayan fitar wani rahoto da ke cewa cikin shekara 1 kaɗai an tattara alƙaluman sabbin mutum dubu 6 da aka gano suna ɗauke da cutar. Wannan cuta mai alaƙa da nau’in jini, na daga cikin matakan yaƙi da ita shi ne tabbatar da gwaje-gwajen jini tun kafin aure don kaucewa haifar yara masu ɗauke da ita, ganin cewa hanya ɗaya tal ta samun masu cutar shi ne ta hanyar gado wato daga iyaye.
-
Illolin da ke tattare da sauya launin fata da wasu mata ke yi 08.06.2026 10minShirin lafiya Jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan yadda mata suka rungumi tsarin gyaran jiki ta fannoni daban-daban kama daga magungunan sha ko mayukan shafawa ko kuma salon amfani da na’ura da nufin ƙawata sura.
-
Illolin magungunan matsi ga lafiyar mata 01.06.2026 10minShirin a wannan mako zai ɗora ne akan wanda ya gabace shi a makon jiya, sai dai a wannan karon zamu karkata ga illolin da magungunan matsi ke haifarwa ga lafiyar mata, duk da ya ke matan kan yi don bajinta ko nuna isa a wajen mazajensu.
-
Abubuwan da ke haddasa cutuka ga al'aura ko matantaka ga mata 25.05.2026 9minShirin Lafiya Jari ce na wannan makon ya yi nazari kan ƙaruwar matan da ke fama da cutuka masu alaƙa da al’aura ko kuma matantaka, tare da laluben hanyoyin magancesu ta hanyar tattaunawa da ƙwararru a wannan fanni, cutukan da ƙwararrun ke alaƙantawa da rashin baiwa al’aurar kariya wanda a lokuta da dama ke haddasa gagarumar matsala.
-
Abubuwan da ya kamata a sani kan sabuwar cutar Hantavirus da ta ɓulla 18.05.2026 10minShirin Lafiya Jari Ce a wannan makon ya yi nazari kan cutar Hantavirus da duniya ta ga ɓullarta a baya-bayan nan, lamarin da ya sanya fargaba a zuƙatan jama’a, musamman ganin yadda ake alaƙanta wannan cuta a sahun masu haɗari da tarihi ya nuna yaddda suka yiwa duniya ɓarna matuƙa.
-
Yadda ake gudanar da yaƙi da cutar polio tsakanin Nijar da maƙwaftanta 11.05.2026 9minShirin lafiya jari Ce a wannan makon zai nazarci yadda ake gudanar aikin yaki da cutar polio tsakanin ƙasashen makwabtan juna wato Najeriya da Nijar a wani yunƙuri na kakkaɓe ɓurɓushin wannan cuta musamman a yankunan kan iyaka na ƙasashen biyu duk kuwa da saɓanin diflomasiyyar da ke tsakanin gwamnatocin ƙasashen biyu.
-
Wani bincike ya gano yadda kashi 13 na al'ummar Ghana ke rayuwa cutar ƙoda 04.05.2026 9minA wannan makon shirin na Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir Aminu ya yi nazari kan wani bincike can a Ghana da ke ƙiyasta cewa kusan kashi 13.3 na yawan jama’ar ƙasar na rayuwa da cutukan ƙoda, galibi ba tare da masaniyar suna ɗauke da ita ba, lura da yadda cutar bata nuna alamu a farko har sai ta kai ga ta’azzara.
-
Yadda tsananin zafin bana ke barazana ga lafiyar jama’a a Arewa 27.04.2026 10minA wannan makon, shirin na Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan tsananin zafin da ake fuskanta a wasu jihohi na yankin Arewacin Najeriya, wanda masana suka yi ittifaƙin ya kai matakin da ka iya haddasa wasu cutuka ko kuma tayar da kwantattu.
-
An samu raguwar haihuwa a Najeriya sakamakon rungumar tsarin tazarar Iyali 20.04.2026 10minShirin Lafi Jari ce a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba ne kan wani rahoton sashen bincike da kula da lafiyar jama’a na NDHS da ke ƙarƙashin hukumar kula da yawan jama’a ta Najeriya NPC, wanda ke nuna cewa daga shekarar 2024 yawan haihuwa ya ragu matuƙa tsakan matan Najeriya daga kashi 5.3 zuwa kashi 4.8.
-
Yadda Cutar Sankarau ke barazana ga wasu ƙasashen yammacin Afirka 13.04.2026 9minShirin Lafiya Jari ce a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba ne kan cutar ɗan sanƙarau ko kuma meningitis, cutar da a yanzu haka wasu ƙasashe ke cikin haɗarin fuskantar ɓullarta musamman a yammacin Afrika, waɗanda dama ke a tubalin fuskantar wannan cuta lokaci zuwa lokaci.
-
Kalubalen da ake fuskanta wajan yaki da cutar babban tari ko tuberculosis 06.04.2026 10minShirin Lafiya Jarice na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali gameda tarin matsaloli da gangamin yaki da babban tari ke cin karo dasu.
-
Najeriya ta karɓi sabbin alluran rigakafin cutar HIV 30.03.2026 10minShirin Lafiya Jari ce na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan sabbin alluran rigakafin cutar Sida ko kuma HIV Aids da Najeriya ta karɓa ƙarƙashin shirin yaƙi da wannan cuta mai haɗari.
-
Haɗarin cizon mahaukacin kare da ke haddasa cutar zangai maras jin magani 23.03.2026 9minA wannan makon shirin na lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba kan matsalar cutar zangai ko cizon mahaukacin kare, cutar dake daɗa bazuwa a jamhuriyyar Nijar musaman a Jihar Maradi, jihar dake sahun gaba wajan masu fama da wannan matsala.
-
Jita-jitar dake alaƙanta kamuwa da cututtuka ta hanyar amfani da kayayyakin lantarki 16.03.2026 9minA wannan makon shirin na Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan jita-jitar da ke alaƙanta amfani da wasu kayakin lantarki a matsayin dalilan da ke sabbaba kamuwa da wasu nau’ikan cutuka ciki har da Cancer.A wannan makon shirin na Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan jita-jitar da ke alaƙanta amfani da wasu kayakin lantarki a matsayin dalilan da ke sabbaba kamuwa da wasu nau’ikan cutuka ciki har da Cancer.
-
Cututtukan da ke barazana ga lafiyar jama'a a lokacin azumi 09.03.2026 10minShirin Lafiya Jari ce a wannan makon ya mayar da hankali ne kan irin cututtuka da ke barazana ga lafiyar al'umma a lokacin azumin watan Ramadan, musamman ga masu azumi da ke fuskantar sauye-sauyen lafiyar jiki.
-
Zubar hazo a lokacin zafi ya haddasawa mutane da dama rashin lafiya a Kamaru 02.03.2026 10minA wannan makon shirin na Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan sauyawar yanayin da wani yanki na arewacin ƙasar Kamaru ya gamu da shi a watan Fabarairun da ya gabata wanda ba safai aka saba ganin faruwarsa ba, ta yadda ake ganin zubar hazo a wani yanayi da kuma ake fama da tsananin zafi, wanda ya haddasa cutuka, lamarin da ya sanya gamayyar masana lafiya dana yanayi jan hankali jama’a don su ɗauki matakan baiwa lafiyarsu kariya.
-
Yadda yakamata jama'a su kula da cimakarsu a lokacin azumin Ramadan 23.02.2026 10minShirin Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako zai mayar da hankali kan cimaka a lokacin azumin watan Ramadana, dama yadda wasu ke fuskantar matsaloli masu alaƙa ɓacin ciki sakamakon yanayin ciye-ciyen da akan yi ko dai a lokacin buɗa baki ko kuma sahur.
-
Najeriya ta ƙaddamar da dokar ta ɓaci a harkar kiwon lafiya 02.02.2026 10minA wannan makon shirin zai yi dubi ne kan dokar ta baci a harkan lafiya da gwamnatin Najeriya ta kaddamar inda ta sanar da karuwar cutuka masu alaka da gurbatacciyar iskar da jama’ar ƙasar ke shaka.
-
An fara gangamin rigakafin cutar Typhoid irinsa na farko a Jamhuriyyar Nijar 19.01.2026 9minShirin Lafiya Jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan gangamin rigakafin cutar Typhoid da mahukuntan Jamhuriyyar Nijar suka faro a faɗin ƙasar, irinsa na farko da aka taɓa gani a tarihi a wani yanayi da ake ganin ta’azzarar wannan cuta a ƙasar ta yankin Sahel. Wasu alƙaluman hukumar Lafiyar Jamhuriyyar Nijar a 2021 sun ce mutane dubu 30 suka kamu da cutar, a wancan lokaci wadda ta haddasa mutuwar mutane 400.
-
Illolin da sauyin yanayi ke haifarwa ga lafiyar jama'a 12.01.2026 9minA wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya mayar da hankali ne kan illolin da sauyawar yanayi ke haifarwa ga lafiyar jama’a, musamman ganin yadda hunturu ya fara amma kuma kwatsam ya ɗauke cikin ƙanƙanin lokaci tare da shigowar zahi, lamarin da ya haddasa cutuka masu yawa a tsakanin jama’a.
Suosittu maassa
Tämä podcast esiintyy myös näiden maiden podcast-listoilla.