Al'adun Gargajiya
RFI Hausa
0
Shirin yana kawo al'adun gargajiya na zamani da na da daga sassan duniya, yana nuna bambancin al'adu da yawan jama'a. Akwai kuma shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da ake gabatarwa a ranakun Asabar da Lahadi.
Episodi
-
Yadda kiɗan Gurmi ke neman ɓacewa a ƙasar Hausa 16.06.2026 9minShirinmu na yau ya leƙa sassan arewacin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, tare da duba yadda wani fitaccen kiɗan gargajiya, wato kiɗan Gurmi, ke fuskantar barazanar bacewa a fadin ƙasar Hausa. Shin me ke janyo haka, kuma wane canji fasahar zamani ta kawo?
-
Yadda Hausawa mazauna Jamus suka gudanar da gagarumin taron sada zumunci 09.06.2026 10minShirin Al'adun mu na Gado na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda Hausawa mazauna Jamus suka gudanar da wani gagarumin taro.
-
Gombe: Fulani sun yi taro kan warware matsalolin da ke ɓata musu suna 28.05.2026 10minShirin Al'adunmu na Gado a wannan mako, yayi tattaki ne zuwa garin Gombe, inda Al'ummar Fulani suka gudanar da wani taro na farfaɗo da Al'adunsu na Gargajiya, da kuma tattaunawa a kan hanyoyin da za a bi wajen maido da Tarbiyya, gami da zamantakewa kyakkyawa a tsakanin Fulanin da kuma sauran Ƙabilu.
-
Yadda al'ummar wani gari suka riƙe Al'adar da suke kira da "Sai kowa ya zo" 12.05.2026 10minShirin Al'adunmu na Gado na wannan mako tare da Abdoulaye Issa ya yi duba kan wata Al'ada da ake kira "sai kowa ya zo" a tsakanin al'ummar wani gari da ke Yankin Arewacin Najeriya.
-
Tasirin karance-karance Littattafan Hausa wajen ɗabbaƙa al'adun Hausawa 05.05.2026 11minShirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya mayar da hankali ne kan tasirin karance-karancen Littattafan Hausa a zamantakewar Al'ummar yankin.
-
Rawar da mayaƙa suka taka zamanin da a Masarautun ƙasar Hausa 21.04.2026 10minShirin Al’adun mu na Gado a wannan makon ya leka Jamhuriyar Nijar ne, inda ya duba batun da ya shafi mazajen dauri, musaman mayaƙan gargajiya a wannan zamani, jaruman da ke ƙarƙashin inuwar sarakunan gargajiya.
-
Yadda kiɗan shantu ke ƙoƙarin ɓacewa duk da shaharar da ya yi a shekarun baya 07.04.2026 10minShirin Al'adun mu na gado na wnnann mako ya waiwayi kiɗan Shantu ne da ya shahara tsakanin Mata a shekarun baya, wanda bayan tasirin da ya yi a waccan lokaci a fagen nishaɗantarwa, kiɗan na Shantu ke neman ɓacewa a yanzu. A shekarun baya dai wannan kiɗa na Shantu ya shahara ne tsakanin mata a yankunan arewacin Najeriya musamman a makarantu ko ɗalibai da kuma wasu sassan Jamhuriyar Nijar.
-
Yadda bikin addinin gargajiya na Vodun ke gudana a Jamhuriyar Benin (2) 27.01.2026 10minShirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya ɗora ne a kan yadda aka gudanar da bukukuwan addinin gargajiya na Vodun a Jamhuriyyar Benin, bikin addinin gargajiya da ke da muhimmanci a ƙasar.
-
Yadda bikin addinin gargajiya na Vodun ke gudana a Jamhuriyar Benin 20.01.2026 10minShirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya yi tattaki ne zuwa Jamhuriyar Benin, inda ya halarci bukukuwan addinin gargajiya na Vodun, bikin da ke da muhimmanci matuƙa a ƙasar.
-
Hausawan Turai na fuskantar barazanar ɓacewar harshe da al'adunsu 13.01.2026 10minShirin "Al'adunmu na gado" a wannan makon tare da Nura Ado Suleiman ya leƙa ne Masarautar Hausawa da ke nahiyar Turai, inda a makon Masarautar ta karɓi baƙuncin Mai Martaba Sarkin Daura Dakta Umar Faruk Umar da ya yi tattaki daga Tarayyar Najeriya, domin halartar bikin karrama Sarkin Hausawan na Turai da kuma naɗin wasu sabbin muƙaman na sarauta da suka shafi sassan nahiyar.
-
Yadda aka gudanar da bikin nuna al'adu na masarautar Jiwa a Abuja 06.01.2026 9minShirin Al'adun gargajiya na wanan makon tare da Abdoulaye Issa ya yi duba game da yadda aka gudanar da bikin al'adu na masarautar Jiwa a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
-
Yadda aka gudanar da bikin naɗin sarautar sarkin Komadugu a Maraɗi 02.12.2025 9minShirin na yau ya yada zango jihar Diffa dake Jamhuriyar Nijar,yankin da aka gudanar da bikin nadin sabon sarkin Komadugu, wanda ya samu halartar baƙi daga ciki da wajen ƙasar.
-
Yadda sana'ar sassaƙar Turmi ke fuskantar koma baya sabida ci gaban zamani 25.11.2025 9minShirin "Al'adun mu na Gado" na wannan makon ya yi duba ne akan sana'ar nan ta sassaƙar Turmin, wadda ke a matsayin sana'ar al'adun gargajiya, ko da yake a yanzu samar da na'urori da ke amfanin da Turmin keyi ya mayar da sana'ar baya matuka gaya.
-
Yadda ƴan siyasa ke katsalandan a harkokin masarautu a Najeriya 18.11.2025 8minShirin al'adun mu na gado na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda ƴan siyasa ke katsalandan a masarautun gargajiya a Najeriya.
-
Bikin Kalankuwar farfaɗo da al'adun Hausawa a jihar Kano ta Najeriya 04.11.2025 10minShirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ne kan Kalankuwar farfaɗo da al'adunmu Hausawa a jihar Kano ta arewacin Najeriya, a wani yanayi da al'umma ke fuskantar matsalar gushewar tarin al'adu a mataki daban-daban.
-
Yadda al'adar ''Ƴar zaman Ɗaki'' ta zama tarihi tsakanin hausawa 28.10.2025 10minShirin Al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda sananniyar al'adar nan ta zaman ɗaki ke ƙoƙarin shuɗewa tsakanin al'ummar Hausawa.
-
Yadda aka gudanar da bikin makiyaya na Cure Salee a Jamhuriyar Nijar 21.10.2025 9minShirin a wannan mako ya yi tattaki ne, zuwa ƙauyen Ingal da ke Yankin Agadez a jamhuriyyar Nijar, domin waiwayar gagarumin bikin makiyaya da ƙabilu daban-daban da ake yi wa laƙabi da 'Cure Salee' wanda aka saba yi duk shekara. Bikin makiyayan na Cure Salee ya gudana ne a tsakanin ranakun 4 zuwa 6 ga watan da muke ciki na Oktoba. Manufar bikin ita ce yadda za a ƙarfafa haɗin kai tsakanin makiyaya domin kafa ginshiƙin zaman lafiya mai ɗorewa a tsakanin ƙabilu. Bikin na bana ya samu halattar ƙabilun Fulani da na Abzinawa da Larabawa a Nijar ɗin da wasu daga Najeriya, da Mali da burkina Faso da kuma Aljeriya.
-
Yadda sana'ar kaɗi ke gab da gushewa tsakanin al'ummar Hausawa 14.10.2025 10minShirin al'adunmu na gado tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon ya mayar da hankali ne kan gushewar sana'ar kaɗi a ƙasar Hausa duk da kasancewarta guda cikin sana'o'in Hausawan suka gada kaka da kakanni.
-
Banbanci tsakanin maita da tsafi a mahangar al'adu da addini 07.10.2025 10minShirin Al'adunmu na Gado tare da Nura Ado Suleiman a wannan mako, ya mayar da hankali kan manufar Maita da kambun baka a mahangar al'adu da kuma addini, a wani yanayi da ake yiwa wannan abubuwa biyu mabanbantan kallo.
-
Yadda aka bar baya da ƙura a girmamawar da ka yiwa Rarara da digirin Dakta 23.09.2025 10minShirin Al’adunmu na Gargajiya tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon ya sake waiwayar fagen Waƙa guda daga cikin fannoni masu tasiri a Adabin Harshen Hausa la’akari da gudunmawar waƙoƙin da kuma mawaƙan da ke rera su wajen bunƙasa harshen.
Popolare in
Questo podcast compare anche nelle classifiche dei podcast di questi paesi.