Dandalin Fasahar Fina-finai

Dandalin Fasahar Fina-finai

RFI Hausa
Paese Nigeria
Generi Notizie
Lingua HA
Episodi 24
Ultimo 20.06.2026

Fili ne na musamman kan Fina-finai ta hanyar tattauna da masu ruwa da tsaki a wannan fanni a duniya, Tare da wayar wa ma su sauraro kai da kara masu basira dangane da hikimar da Allah ya bai wa wasu ta fanin shirya fim ko tsara wasan kwaikwayo. Wanda ke zo maku a duk ranar Asabar da safe, tare da maimaici a ranar Lahadi da yamma.

Episodi

  • Tattaunawa ta musamman da mashiryin Fina-finai Abdul Amart 20.06.2026 20min
    A cikin shirin na wannan mako za ku ji mu ɗauke da tattaunawa ta musamman da mashiryin Fina-finai Abdul Amart.Muna tafe da batu kan fina-finan da aka fi tafka muhawara akan su cikin mako da muke bankwana da shi. Akwai mu da tattaunawa da Dauda Kahutu Rarara, wanda ya ballo sabuwar Dambarwa da mawaƙi Davido, da kuma yadda yake ganin wakokinsa na siyasa ka iya tasiri a zabe mai zuwa.
  • Karancin ingantaccen labarin fina-finai, lamarin da ke karya darajar su a Najeriya 16.11.2024 20min
    A cikin shirin na wannan mako a bangaren mu na Kannywood zamu duba yadda karancin ingantaccen labarin fina-finai, lamarin da ke karya darajar fina-finan. Za ku ji mu tafe da dambarwar da ta kunno kai tsakanin fitaccen mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara, da hukumar tace fina-finai ta jijar Kano.
  • Korafe-korafen makallata fina-finan Hausa 13.07.2024 20min
    A cikin shirin na wannan mako, zamu sake yin waiwaye kan korafe-korafen makallata fina-finan Hausa, kan yadda mashirya fina-finai suka fi mayar da hankali kan soyayya, tare da fatali da sauran fannonin rayuwa. Za mu tsallaka Jamhuriyar Nijar, inda zamu duba yadda zamani yayi tafiyar ruwa da wake-waken ‘yan mata da ke tashe a baya. Muna tafe da tattaunawa da Hadiza Gire, guda daga cikin matan da suka yi tashe a jamhuriyar Nijar lokacin da suke fagen rera wakokin ‘yan mata.
  • Ko ana 'kan ta waye' a masana'antar Kannywood? 06.02.2022 20min
    Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' ya yi nazari ne a kan al'amarin nan da ake kira 'kan-ta-waye'. Shirin ya yi  bayani a kan menene 'kan-ta-waye', sannan ya tattauna da baki, wadanda suka fadada bayanin don fahimtar mai sauraro.
  • Rayuwar mata masu shirya fina-finai a Nollywood a Najeriya 30.01.2022 20min
    A cikin wannan shirin na dandalin fasahar Fina-finai,Hawa Kabir ta samun tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Duniyar fina-finai dangane da makomar mata musaman a gidajen mazan su,ko wandada ke da niyar yin aure.
  • Halin da masana'antar Fim ta shiga a makon da ya kare 09.01.2022 20min
    Kamar yadda aka saba kowane mako shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai tare da Hauwa Kabeer ya tattauna akan wasu daga cikin muhimman al'amuran da ke wakana a masana'antar fina-fina da ke arewaci da kuma kudancin Najeriya.
  • Abinda ya wakana cikin kungiyar MOPAN a baya bayan nan 19.12.2021 20min
    Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon tare da Hauwa Kabeer, ya leka kungiyar MOPAN ne domin jin wainar da ake toyawa.
  • An kamala zaben wakilan kungiyar yan Fim a jihar Kaduna 12.12.2021 19min
    A cikin shirin duniyar fina-finai,Hawa Kabir ta samu tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harakar fim yan lokuta bayan kamala zaben wakilan MOPAN a jihar Kaduna. Makomar duniyar Fim,hanyoyin kawo karshen baraka a wannan duniya na daga cikin manyan batutuwa da Hawa ta samu tattaunawa da bakin na ta.
  • Fitaccen makawaki ya sha alwashin daukar nauyin tallafawa mata da sana'o'i 05.12.2021 19min
    Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon tare da Hauwa Kabeer ya tattauna da wani fitaccen mawakin Hausa da ya sha alwashin daukar nauyin tallafawa mata da sana'o'i.
  • An fara daukar shirin 'Gidan Badamasi' zango na 4 21.11.2021 20min
    Shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai ya leka inda ake daukar shirin barkwancin nan mai dogon zango, wato 'Gidan Badamasi', inda ya gana da jarumai da masu ruwa da tsaki a shirin, cikin su har da babban daraktan shirin, Falalu Dorayi.
  • Rayuwar Alhaji Umaru Danjuma Katsina da aka fi sani da Kasagi 07.11.2021 20min
    Kasagi wanda ya rubuta fitaccen littafin da aka yi wa suna ‘Kulba na Barna’ ya rasu ne sakamakon gajeruwar rashin rashin lafiya. Danjuma Katsina na daya daga cikin fitattun masu wasan kwaikwayon da suka yi suna daga shekarar 1980 tare da wasu abokan aikin sa a lokacin irin su Kasimu Yero da Tumbuleke da Malam Mamman da karkuzu Na Bodara da kuma Samanja Mazan Fama.
  • Masu ruwa da tsaki kan rubutun adabi da fina-finai na alhinin rasa Kasagi 31.10.2021 20min
    Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon tare da Hauwa Kabir ya tattauna na masu ruwa da tsaki kan rubutun adabin Hausa da kuma fina finai kan rasuwar marigayi Umaru Danjuma Katsina da aka fi sani da Kasagi.
  • Taron kara wa juna sani kan habaka harshen Hausa 2/2 24.10.2021 20min
    Shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai tare da Hauwa Kabir ya cigaba da tattaunawa ne kan taron kara wa juna sani kan habaka harshen Hausa na kungiyar WTC da ya gudana a garin Zaria, dake jihar Kaduna.
  • Taron kara wa juna sani kan habaka harshen Hausa 03.10.2021 20min
    A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai, hauwa Kabir ta leka taron kara wa juna sani kan habaka harshen Hausa na kungiyar WTC  da ya gudana a Zaria, jihar Kaduna. Shirin ya gana da shehunan malaman da suka halarci taron. 
  • Rayuwar yan wasan fina-finai a Tarrayar Najeriya 26.09.2021 20min
    A cikin shirin dandalin Fina-finai,Hawa Kabir ta jiyo ta bakin  masu shirya fim a Nollywood,wanda suka kuma yi mata bayyana dangane da rayuwar su da kuma irin wasannin da suke iya kasancewa a cikin su ga baki daya.
  • Gudunmawar Ahmad Aliyu Tage ga masana'antar Kannywood 19.09.2021 20min
    Shirin dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon ya tattauna kan rashin da masana'antar Kannywood tayi na wasu manyan jaruman ta, musamman Ahmad Aliyu Tage da ya rasu a makon da ya gabata.
  • Ta'aziyyar mawakin siyasa Isyaku Forest 12.09.2021 20min
    Shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai' na wannan mako tare da Hauwa Kabir ya kawo mana ta'aziyyar mawakin siyasan nan, Isyaku Forest, wanda ya rasu kwanan nan. Hauwa Kabir ta tattauna da makusanta da aminansa, ciki har da shahararren mawakin siyasa, Rarara.
  • Dalilan da suka haifar da koma baya ga kasuwar fina-finan Hausa 05.09.2021 20min
    Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon ya tattauna da masu ruwa da tsaki kan dalilan da suka janyo faduwar kasuwa fina-finan Hausa.
  • Mutane na yi wa fim kallon hadarin kaji don ba su ke yi ba - Isa Bello Ja 29.08.2021 20min
    A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' Hauwa kabir ta kawo abubuwa da dama a bangaren fina-finai, inda ta duba yadda yanzu masana'antar Kannywood ke gogayya da takwararta tav kudancin Najeriya. Ta kuma tattauna da shugaban jaruman Kannywood, Alhassan Kwale wanda ya ce Umma Shehu da Sadiya Haruna ba 'yan Kannywood bane.
  • Tattaunawa da Yaya Dankwambo na shirin gidan Badamasi 22.08.2021 20min
    Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon tare da Hauwa Kabeer ya tattauna da Muhammadu Nura Yakubu da a yanzu aka fi sani da sunan Yaya Dankwambo na shirin fim din Gidan Badamasi.

Popolare in

Questo podcast compare anche nelle classifiche dei podcast di questi paesi.