Al'adun Gargajiya

Al'adun Gargajiya

RFI Hausa
Țara Franța
Genuri Știri
Limba HA
Episoade 24
Ultimul 14.07.2026

Shirin yana kawo al'adun gargajiya na zamani da na da daga sassan duniya, yana nuna bambancin al'adu da yawan jama'a. Akwai kuma shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da ake gabatarwa a ranakun Asabar da Lahadi.

Episoade

  • Muhimmancin zurfafa bincike a dukkan fannoni gabanin aure 14.07.2026 10min
    Shirin 'Al'adunmu Na Gado zai yi duba ne kan muhimmancin zurfafa bincike gabanin aure.  Al’adun al’ummar Hausawa da ma mafi yawan al’ummomin da ke zaune a yankin arewacin Nigeria, sun sahale wa iyaye, gudanar da bincike kan yaron da ya nuna kai yana son ‘yarsu da aure, kamar yadda shima bangaren angon, kan yi bincike kan yanayin lafiya, tarbiyya da nasabar yarinyar.
  • Makomar makarantun gwaji na harsunan gida a Jamhuriyar Nijar. 30.06.2026 11min
    Shirin wannan makon zai duba makomar makarantun gwaji na harsuna  gida da suka haɗa harshen Hausa. A waɗannan makarantu, za a riƙa koyarwa da harsunan gida.  Za a koya wa yara sana'o'i irin na gargajiya, a kuma koya musu adabin harsshe da sauransu.
  • Yadda Hausawa ke cin kasuwar abincin gargajiya a Saudiyya 23.06.2026 9min
    Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoullaye Issa a wannan mako ya yi duba kan yadda Hausawa ke ɗabbaƙa al'adunsu ta hanyar hada-hadar abincin gargajiya a ƙasa mai tsarki ko kuma Saudi Arabiya.
  • Yadda kiɗan Gurmi ke neman ɓacewa a ƙasar Hausa 16.06.2026 9min
    Shirinmu na yau ya leƙa sassan arewacin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, tare da duba yadda wani fitaccen kiɗan gargajiya, wato kiɗan Gurmi, ke fuskantar barazanar bacewa a fadin ƙasar Hausa. Shin me ke janyo haka, kuma wane canji fasahar zamani ta kawo?
  • Yadda Hausawa mazauna Jamus suka gudanar da gagarumin taron sada zumunci 09.06.2026 10min
    Shirin Al'adun mu na Gado na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda Hausawa mazauna Jamus suka gudanar da wani gagarumin taro.
  • Gombe: Fulani sun yi taro kan warware matsalolin da ke ɓata musu suna 28.05.2026 10min
    Shirin Al'adunmu na Gado a wannan mako, yayi tattaki ne zuwa garin Gombe, inda Al'ummar Fulani suka gudanar da wani taro na farfaɗo da Al'adunsu na Gargajiya, da kuma tattaunawa a kan hanyoyin da za a bi wajen maido da Tarbiyya, gami da zamantakewa kyakkyawa a tsakanin Fulanin da kuma sauran Ƙabilu.
  • Yadda al'ummar wani gari suka riƙe Al'adar da suke kira da "Sai kowa ya zo" 12.05.2026 10min
    Shirin Al'adunmu na Gado na wannan mako tare da Abdoulaye Issa ya yi duba kan wata Al'ada da ake kira "sai kowa ya zo" a tsakanin al'ummar wani gari da ke Yankin Arewacin  Najeriya.
  • Tasirin karance-karance Littattafan Hausa wajen ɗabbaƙa al'adun Hausawa 05.05.2026 11min
    Shirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya mayar da hankali ne kan tasirin karance-karancen Littattafan Hausa a zamantakewar Al'ummar yankin.
  • Rawar da mayaƙa suka taka zamanin da a Masarautun ƙasar Hausa 21.04.2026 10min
    Shirin Al’adun mu na Gado a wannan makon ya leka Jamhuriyar Nijar ne, inda ya duba batun da ya shafi mazajen dauri, musaman mayaƙan gargajiya a wannan zamani, jaruman da ke ƙarƙashin inuwar sarakunan gargajiya. 
  • Yadda kiɗan shantu ke ƙoƙarin ɓacewa duk da shaharar da ya yi a shekarun baya 07.04.2026 10min
    Shirin Al'adun mu na gado na wnnann mako ya waiwayi kiɗan Shantu ne da ya shahara tsakanin Mata a shekarun baya, wanda bayan tasirin da ya yi a waccan lokaci a fagen nishaɗantarwa, kiɗan na Shantu ke neman ɓacewa a yanzu. A shekarun baya dai wannan kiɗa na Shantu ya shahara ne tsakanin mata a yankunan arewacin Najeriya musamman a makarantu ko ɗalibai da kuma wasu sassan Jamhuriyar Nijar.
  • Yadda bikin addinin gargajiya na Vodun ke gudana a Jamhuriyar Benin (2) 27.01.2026 10min
    Shirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya ɗora ne a kan yadda aka gudanar da bukukuwan addinin gargajiya na Vodun a Jamhuriyyar Benin, bikin addinin gargajiya da ke da muhimmanci a ƙasar.
  • Yadda bikin addinin gargajiya na Vodun ke gudana a Jamhuriyar Benin 20.01.2026 10min
    Shirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya yi tattaki ne zuwa Jamhuriyar Benin, inda ya halarci bukukuwan addinin gargajiya na Vodun, bikin da ke da muhimmanci matuƙa a ƙasar.
  • Hausawan Turai na fuskantar barazanar ɓacewar harshe da al'adunsu 13.01.2026 10min
    Shirin "Al'adunmu na gado" a wannan makon tare da Nura Ado Suleiman ya leƙa ne Masarautar Hausawa da ke nahiyar Turai, inda a makon Masarautar ta karɓi baƙuncin Mai Martaba Sarkin Daura Dakta Umar Faruk Umar da ya yi tattaki daga Tarayyar Najeriya, domin halartar bikin karrama Sarkin Hausawan na Turai da kuma naɗin wasu sabbin muƙaman na sarauta da suka shafi sassan nahiyar.
  • Yadda aka gudanar da bikin nuna al'adu na masarautar Jiwa a Abuja 06.01.2026 9min
    Shirin Al'adun gargajiya na wanan makon tare da Abdoulaye Issa ya yi duba game da yadda aka gudanar da bikin al'adu na masarautar Jiwa a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
  • Yadda aka gudanar da bikin naɗin sarautar sarkin Komadugu a Maraɗi 02.12.2025 9min
    Shirin na yau ya yada zango jihar Diffa dake Jamhuriyar Nijar,yankin da aka gudanar da bikin nadin sabon sarkin Komadugu, wanda ya samu halartar baƙi daga ciki da wajen ƙasar.
  • Yadda sana'ar sassaƙar Turmi ke fuskantar koma baya sabida ci gaban zamani 25.11.2025 9min
    Shirin "Al'adun mu na Gado" na wannan makon ya yi duba ne akan sana'ar nan ta sassaƙar Turmin, wadda ke a matsayin sana'ar al'adun gargajiya, ko da yake a yanzu samar da na'urori da ke amfanin da Turmin keyi ya mayar da sana'ar baya matuka gaya. 
  • Yadda ƴan siyasa ke katsalandan a harkokin masarautu a Najeriya 18.11.2025 8min
    Shirin al'adun mu na gado na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda ƴan siyasa ke katsalandan a masarautun gargajiya a Najeriya.
  • Bikin Kalankuwar farfaɗo da al'adun Hausawa a jihar Kano ta Najeriya 04.11.2025 10min
    Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ne kan Kalankuwar farfaɗo da al'adunmu Hausawa a jihar Kano ta arewacin Najeriya, a wani yanayi da al'umma ke fuskantar matsalar gushewar tarin al'adu a mataki daban-daban.
  • Yadda al'adar ''Ƴar zaman Ɗaki'' ta zama tarihi tsakanin hausawa 28.10.2025 10min
    Shirin Al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda sananniyar al'adar nan ta zaman ɗaki ke ƙoƙarin shuɗewa tsakanin al'ummar Hausawa.
  • Yadda aka gudanar da bikin makiyaya na Cure Salee a Jamhuriyar Nijar 21.10.2025 9min
    Shirin a wannan mako ya yi tattaki ne, zuwa ƙauyen Ingal da ke Yankin Agadez a jamhuriyyar Nijar, domin waiwayar gagarumin bikin makiyaya da ƙabilu daban-daban da ake yi wa laƙabi da 'Cure Salee' wanda aka saba yi duk shekara. Bikin makiyayan na Cure Salee ya gudana ne a tsakanin ranakun 4 zuwa 6 ga watan da muke ciki na Oktoba. Manufar bikin ita ce yadda za a ƙarfafa haɗin kai tsakanin makiyaya domin kafa ginshiƙin zaman lafiya mai ɗorewa a tsakanin ƙabilu. Bikin na bana ya samu halattar ƙabilun Fulani da na Abzinawa da Larabawa a Nijar ɗin da wasu daga Najeriya, da Mali da burkina Faso da kuma Aljeriya.

Popular în

Acest podcast apare și în topurile de podcasturi din aceste țări.