Al'adun Gargajiya
RFI Hausa
0
Shirin yana kawo al'adun gargajiya na zamani da na da daga sassan duniya, yana nuna bambancin al'adu da yawan jama'a. Akwai kuma shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da ake gabatarwa a ranakun Asabar da Lahadi.
Episodes
-
Yadda Hausawa ke gudanar da sana'ar Fawa a ƙasar Togo 11.11.2026 9mShirin 'Al'adunmu na Gado' tare da Abdoulaye Issa ya sake leƙawa ƙasar Togo a wannan mako, inda ya duba yadda Hausawa ke gudanar da sana'ar Fawa. -
Mahukunta na yunkurun sake rubuta tarihin Jamhuriyyar Nijar 27.10.2026 9mShirin Al'adun Mu Na Gado na wannan mako yayi duba ne kan yunƙurin sake rubuta tarihin Jamhuriyyar Niger da magabatan ƙasar suka dauri aniyar yi. Tun bayan juyyin milki da sojojin ƙasar Niger suka yi da niyar raba gari da suka yi da duk wani gadon Turawan mulkin mallaka da suka mullaki ƙasar, sun ga dacewar sake rubuta tarihin ƙasar domin galibinshi tarihi ne da Turawan suka rubuta abinda yayi musu, wanda wani lokacin ma ba gaskiya bane ko kuma an masa gyaran fuska. -
Yadda al'ummar Hausawa kusan dubu 30 ke rayuwa a tsakanin ƙabilun ƙasar Togo 20.10.2026 9mShirin al’adun mu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan karon ya leka ƙasar Togo ne, inda muka yi ƙoƙarin jin yadda Hauasawan wannan ƙasa ke rayuwa. A Togo dai akwai kimanin Hasauwa dubu 30 da ke rayuwa da sauren ƙabilun wannan ƙasa ba tareda wata matsala, dai dai gwalgwado dangantaka na tafiya tsakanin su ba tareda an fuskanci wata matsala. -
Bikin al'adun makiyaya na ƙasa a Jamhuriyar Nijar 13.10.2026 9m'Al’adunmu Na Gado' na wannan mako tare da Nura Ado Suleiman ya sake yin tattaki ne zuwa garin Ingal da ke Yankin Agadez a Jamhuriyyar Nijar, inda aka gudanar da bikin ala’adu na ƙasa baki ɗaya da ke haɗa makiyaya daga ƙabilu daban-daban da ake yi wa laƙabi da 'Cure Salee'. An dai saba gudanar da bikin makiyayan ne a kowane makon farko na cikin watan Oktoba, da zummar ƙarfafa haɗin kai tsakanin makiyaya don zaman lafiya mai ɗorewa a tsakanin ƙabilu. -
Mahukuntan Nijar sun karrama fitaccen mawaƙin gargajiya Mamman Gawo Filinge 06.10.2026 10mDa yake mawaƙan gargajiya na da matuƙar tasiri a ƙasar Hausa, mahukunta sun karrama fitaccen mawaƙin Nijar, Marigayi Alhaji Mamman Gawo Filinge, inda aka raɗawa wani titi sunansa. -
Jamhuriyar Nijar ta gudanar da bikin ranar Hausa ta bana a ƙasar 15.09.2026 10mShirin Al’adumu na gado a wannan makon ya sake waiwayar baukukuwan ranar Hausa ne ta Duniya, ranar da babban taronta ke gudana a dukkanin ranakun 26 ga watan Agusta duk shekara, to amma kasancewar bikin ya samu karɓuwa a gwamman ƙasashe ya sa bayan babban taron ake gudanar da wasu ƙarin bukukuwan ranar hausar ta Duniya a ƙasashe daban daban, ciki har da Jamhuriyar Nijar, inda aka gudanar da bikin zagayowar ranar hausar ta Duniya a ranar 8 ga watan Satumban da muke. -
Muhawara kan banbance tsakanin ƙabilun Hausawa da kuma Fulani a Najeriya 08.09.2026 9mShirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya mayar da hankali kan zamantakewa da auratayyar ƙabilun Hausawa da Fulani, ƙabilu 2 da suka juye zuwa Hausa Fulani bayan zaman tare na tsawon shekaru musamman a Najeriya. -
Batutuwan da bikin 'Ranar Hausa ta Duniya' zai mayar da hankali kai a bana 25.08.2026 10mShirin Ala'adunmu na gado a wannan mako ya mayar da hankali ne kan 'Ranar Hausa ta Duniya' 'lokaci na musamman da ake amfani da shi wajen tunatar da muhimmancin harshen Hausa da kuma Al’adun Hausawa. -
Halin da ake ciki game da al'adar 'Yan Kama da ke neman ɓacewa a ƙasar Hausa 18.08.2026 10mShirin "Al’adunmu na gado, ya mayar da hankali kan fadi-tashin da ake yi don adana tsohuwar al'adar mawaƙan 'Yan Kama a ƙasar Hausa. -
Wane tasiri Chamfi ke da shi wajen gyarawa ko kuma ruguza aure musamman a zamanin baya 04.08.2026 10mShirin Al'adunmu na gado na wannan mako zai mayar da hankali ne kan yadda Chamfe-Chamfe ke shafar lamuran auratayya musamman a zamanin baya. -
Muhimmancin zurfafa bincike a dukkan fannoni gabanin aure 14.07.2026 10mShirin 'Al'adunmu Na Gado zai yi duba ne kan muhimmancin zurfafa bincike gabanin aure. Al’adun al’ummar Hausawa da ma mafi yawan al’ummomin da ke zaune a yankin arewacin Nigeria, sun sahale wa iyaye, gudanar da bincike kan yaron da ya nuna kai yana son ‘yarsu da aure, kamar yadda shima bangaren angon, kan yi bincike kan yanayin lafiya, tarbiyya da nasabar yarinyar. -
Makomar makarantun gwaji na harsunan gida a Jamhuriyar Nijar. 30.06.2026 11mShirin wannan makon zai duba makomar makarantun gwaji na harsuna gida da suka haɗa harshen Hausa. A waɗannan makarantu, za a riƙa koyarwa da harsunan gida. Za a koya wa yara sana'o'i irin na gargajiya, a kuma koya musu adabin harsshe da sauransu. -
Yadda Hausawa ke cin kasuwar abincin gargajiya a Saudiyya 23.06.2026 9mShirin al'adunmu na gado tare da Abdoullaye Issa a wannan mako ya yi duba kan yadda Hausawa ke ɗabbaƙa al'adunsu ta hanyar hada-hadar abincin gargajiya a ƙasa mai tsarki ko kuma Saudi Arabiya. -
Yadda kiɗan Gurmi ke neman ɓacewa a ƙasar Hausa 16.06.2026 9mShirinmu na yau ya leƙa sassan arewacin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, tare da duba yadda wani fitaccen kiɗan gargajiya, wato kiɗan Gurmi, ke fuskantar barazanar bacewa a fadin ƙasar Hausa. Shin me ke janyo haka, kuma wane canji fasahar zamani ta kawo? -
Yadda Hausawa mazauna Jamus suka gudanar da gagarumin taron sada zumunci 09.06.2026 10mShirin Al'adun mu na Gado na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda Hausawa mazauna Jamus suka gudanar da wani gagarumin taro. -
Gombe: Fulani sun yi taro kan warware matsalolin da ke ɓata musu suna 28.05.2026 10mShirin Al'adunmu na Gado a wannan mako, yayi tattaki ne zuwa garin Gombe, inda Al'ummar Fulani suka gudanar da wani taro na farfaɗo da Al'adunsu na Gargajiya, da kuma tattaunawa a kan hanyoyin da za a bi wajen maido da Tarbiyya, gami da zamantakewa kyakkyawa a tsakanin Fulanin da kuma sauran Ƙabilu. -
Yadda al'ummar wani gari suka riƙe Al'adar da suke kira da "Sai kowa ya zo" 12.05.2026 10mShirin Al'adunmu na Gado na wannan mako tare da Abdoulaye Issa ya yi duba kan wata Al'ada da ake kira "sai kowa ya zo" a tsakanin al'ummar wani gari da ke Yankin Arewacin Najeriya. -
Tasirin karance-karance Littattafan Hausa wajen ɗabbaƙa al'adun Hausawa 05.05.2026 11mShirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya mayar da hankali ne kan tasirin karance-karancen Littattafan Hausa a zamantakewar Al'ummar yankin. -
Rawar da mayaƙa suka taka zamanin da a Masarautun ƙasar Hausa 21.04.2026 10mShirin Al’adun mu na Gado a wannan makon ya leka Jamhuriyar Nijar ne, inda ya duba batun da ya shafi mazajen dauri, musaman mayaƙan gargajiya a wannan zamani, jaruman da ke ƙarƙashin inuwar sarakunan gargajiya. -
Yadda kiɗan shantu ke ƙoƙarin ɓacewa duk da shaharar da ya yi a shekarun baya 07.04.2026 10mShirin Al'adun mu na gado na wnnann mako ya waiwayi kiɗan Shantu ne da ya shahara tsakanin Mata a shekarun baya, wanda bayan tasirin da ya yi a waccan lokaci a fagen nishaɗantarwa, kiɗan na Shantu ke neman ɓacewa a yanzu. A shekarun baya dai wannan kiɗa na Shantu ya shahara ne tsakanin mata a yankunan arewacin Najeriya musamman a makarantu ko ɗalibai da kuma wasu sassan Jamhuriyar Nijar.
Popular in
The podcast also appears in the podcast charts of these countries.