Lafiya Jari ce

Lafiya Jari ce

RFI Hausa
Country Nigeria
Genres Science
Language HA
Episodes 24
Latest 16.11.2026

Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama'a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.

Episodes

  • Ƙalubalen da majinyata ke fustanka na yawan sauya magungunan da likitoci ke musu
    Ƙalubalen da majinyata ke fustanka na yawan sauya magungunan da likitoci ke musu 16.11.2026 10m
    Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon yayi dubu ne kan yadda likitoci ko jami’an lafiya ke sauya magungunan da marasa lafiya suka siyu duk tsadarsu, ko da kuwa ba a kai ga kammala amfani da su ba, wani lamari da ke ciwa majinyata tuwo a ƙwarya.
  • Ƙasashen Afrika na fuskantar barazanar yaɗuwar cutar Ebola
    Ƙasashen Afrika na fuskantar barazanar yaɗuwar cutar Ebola 09.11.2026 10m
    Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon ya yi duba ne kan cutar Ebola da yanzu haka ke barazana ga duniya musamman ƙasashen nahiyar Afrika tun bayan ɓullarta a Jamhuriyyar Congo cikin watan Mayun shekarar nan. Kawo yanzu cutar ta Ebola nau’in Bundibugyo da ba a iya kai ga nasarar samar da magani ko kuma rigakafinta ba, ta kashe mutanen da yawansu ya haura dubu 5 cikin mutum fiye da dubu 10 da suka harbu a Congo, yayinda a ɓangare guda ta fantsama wasu ƙasashen Afrika.
  • Matsalar bijire wa magunguna da ƙwayoyin cuta ke yi a jikin ɗan adam
    Matsalar bijire wa magunguna da ƙwayoyin cuta ke yi a jikin ɗan adam 02.11.2026 10m
    A wannan makon shirin zai yi duba ne kan matsalar Antimicrobial resistance, wato wani yanayi da ake kaiwa ta yadda ƙwayoyin cuta ke bijirewa magunguna a jikin ɗan adama, matsalar da ke ƙoƙarin zama ruwan dare a duniya, wadda kuma wasu alƙaluman hukumar lafiya ke cewa tana sabbaba asarar rayukan aƙalla mutum miliyan guda duk shekara.
  • Jamhuriyar Nijar ta shirya rigakafin cutar farar masassara a sassan ƙasar
    Jamhuriyar Nijar ta shirya rigakafin cutar farar masassara a sassan ƙasar 26.10.2026 9m
    Shirin na lafiya jari ce a wannan mako, zai yi duba ne kan babbar gayyar allurar rigakafin cutar farar masassara ko kuma Yellow fever da kasar Niger ta shirya a wasu jahohi da nufin daƙile yaɗuwar cutar tsakanin jama'arta.
  • Tsadar maganin asibiti ya tilasta wa wasu jama'a komawa amfani da gargajiya
    Tsadar maganin asibiti ya tilasta wa wasu jama'a komawa amfani da gargajiya 19.10.2026 10m
    A wannan makon shirin ya yi nazari kan yadda tsadar maganin asibiti ke tilastawa jama’a karkatawa amfani da magungunan gargajiya, kodayake akwai kiraye-kirayen masana game da illar waɗannan magunguna a mahangar likitanci.
  • Ƙalubalen lafiyar da matsalar birkicewar al'ada ke haifarwa ga mata
    Ƙalubalen lafiyar da matsalar birkicewar al'ada ke haifarwa ga mata 12.10.2026 10m
    Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya yi nazari kan matsalar birkicewar al’ada a tsakanin mata, matsala ce da ke matsayin ruwan dare a wannan zamani lura da cewa kusan dukkanin 1 cikin mata 3 akan iya samunta da wannan matsala wadda kuma ba safai aka fiya mayar da hankali akanta ba, duk kuwa da ƙalubalen hakan ga lafiyar mata.
  • Yawaitar ɓarkewar cutar Diptheria a sassan jihohin Najeriya
    Yawaitar ɓarkewar cutar Diptheria a sassan jihohin Najeriya 05.10.2026 10m
    A wannan makon shirin ya yi duba kan cutar Diptheria, ko kuma mashaƙo, cutar da a baya-bayan nan ake yawan ganin ɓarkewar annobarta a wasu sassa na jihohin Najeriya wadda kuma ke kisan ɗimbin mutane baya ga kwantar da dama a asibitoci, inda wasu alƙaluma ke cewa daga watan Janairu zuwa Agustan shekarar nan mutane dubu 16 da 997 suka kamu da cutar a sassan Najeriya.
  • Rawar da Ungozomar gargajiya ke takawa wajen ceton rai a yankunan karkara
    Rawar da Ungozomar gargajiya ke takawa wajen ceton rai a yankunan karkara 28.09.2026 10m
    Goyon ciki da haihuwa na cikin mayan ƙalubalen Lafiyar da suka addabi ƙasashe masu tasowa irin Najeriya, ta yadda a kowacce rana ake ganin mutuwar ɗimbin mata a lokacin haihuwa ko kuma renon ciki, baya ga tarin jarirai da ke rasa ransu. A irin wannan yanayi galibi Ungozomar gargajiya ke matsayin masu ceto a irin wannan yanayi.
  • Lafiya Jarice: Muhimmancin tazarar haihuwa ga lafiyar uwa da jaririnta
    Lafiya Jarice: Muhimmancin tazarar haihuwa ga lafiyar uwa da jaririnta 21.09.2026 10m
    Bisa ga zubin halittar ɗan adam kowacce mace kan iya haihuwa aƙalla sau 15 zuwa 30 a tsawon rayuwarta, a wani yanayi da ƙasashen Afrika ke sahun gaba wajen yawan haihuwar, kodayake liktoci na jan hankali game da muhimmancin bayar da tazara ko kuma hutu koma taƙaita haihuwar baki ɗaya saboda dalilai na lafiya.
  • Mata dubu 14 ke kamuwa da cutar kansar mahaifa a Najeriya duk shekara-Rahoto
    Mata dubu 14 ke kamuwa da cutar kansar mahaifa a Najeriya duk shekara-Rahoto 14.09.2026 9m
    Shirin Lafiya jari ce na wannan mako ya mayar da hankali ne kan cutar dajin mahaifa da ke addabar mata musamman a Nahiyar Afrika.
  • Illar da ke tattare da shan magani ba tare da shawara ko umarnin likitoci ba
    Illar da ke tattare da shan magani ba tare da shawara ko umarnin likitoci ba 07.09.2026 10m
    Shirin lafiya jari ce a wannan karon ya mayar da hankali kan ɗabi'ar shan magani ba tare da shawara ko umarnin likitoci ba, wanda a turance ake kira Self-medication da kuma illar hakan ga lafiyar jama’a.
  • Yadda cutar damuwa ke zama ruwan dare a tsakanin al'umma
    Yadda cutar damuwa ke zama ruwan dare a tsakanin al'umma 24.08.2026 9m
    A wannan makon shirin na Lafiya Jari ce zai yi duba ne kan lalurar Depression ko kuma damuwa mai tsanani a harshen hausa, cutar da ke ƙoƙarin zama ruwan dare tsakanin al’umma a baya-bayan nan, wataƙila ko saboda yanayi da matsin rayuwa.
  • Yadda wuraren saida magunguna ke samun karbuwa a jamhuriyar Nijar lokacin damuna
    Yadda wuraren saida magunguna ke samun karbuwa a jamhuriyar Nijar lokacin damuna 17.08.2026 10m
    Shirin a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya leƙa jamhuriyyar Nijar inda ya yi dubi kan yadda ake samun kafuwar wuraren saida magunguna birjik musamman a lokaci irin na damuna, wato dai lokacin da ake ganin yawaitar cutuka irin zazzaɓin cizon sabro.
  • Yadda cutar kwalara ta jefa ɗumbin mutane cikin firgici a jihar Bornon Najeriya
    Yadda cutar kwalara ta jefa ɗumbin mutane cikin firgici a jihar Bornon Najeriya 10.08.2026 9m
    A wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan sake ɓarkewar cutar kwalara ko kuma amai da gudawa a jihar Borno, lamarin da ya jefa ɗimbin jama’a a yanayi na matuƙar damuwa damuwa musamman bayan da rahotanni ke cewa an samu yaɗuwar annobar cutar har a yankunan da ake ajje da ɗimbin mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da matsugunansu.
  • Yadda cutar Bilharzia ko Tsagiya ke barazana ga rayuwar ɗimbin ƴan Afirka
    Yadda cutar Bilharzia ko Tsagiya ke barazana ga rayuwar ɗimbin ƴan Afirka 03.08.2026 10m
    A wannan makon shirin na lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba duba kan cutar Schistosomiasis (shustosumayusus) ko Bilharzia koma Snail fever kamar yadda wasu ke kiranta, cutar nan dai da aka fi sani da tsagiya a hausance, cutar alƙaluma ke nuni da cewa kashi 90 cikin 100 na masu kamuwa da ita na a nahiyar Afrika.
  • Yadda farashin magunguna ke tashi a lokacin damuna da aka fi fama da cutuka
    Yadda farashin magunguna ke tashi a lokacin damuna da aka fi fama da cutuka 27.07.2026 9m
    Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako ya yi dubi ne kan yawaitar cututtuka a irin wannan lokaci na damuna, daidai lokacin da bayanai ke nuni da cewa farashin magunguna ya yi tashin gauron zabbi.
  • Yadda gwamnatin Kano ta yi nasarar rage mace-macen mata a lokacin haihuwa
    Yadda gwamnatin Kano ta yi nasarar rage mace-macen mata a lokacin haihuwa 20.07.2026 10m
    Shirin a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan nasarar da jihar Kano ke iƙirarin samu bayan fitar wani rahoto da ke cewa an samu raguwar mace-macen mata a lokacin haihuwa a sassan jihar wadda a baya ke sahun gaba wajen asarar rayukan ɗimbin mata a lokacin haihuwa ko goyon ciki
  • Matsalar ƙarin mahaifa ko fibroids ga lafiyar mata
    Matsalar ƙarin mahaifa ko fibroids ga lafiyar mata 13.07.2026 10m
    Shirin Lafiya Jari Ce a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan cutar ƙaba ko ƙarin mahaifi ko kuma fibroids da ke addabar tarin mata ta yadda da dama ke rayuwa da shi ba tare da sani ba, yayinda wanzuwarsa a mahaifa kan haddasa matsala ga yanayin haihuwa ga matan.
  • Yadda cutar Typhiod ke barazana ga rayuwar miliyoyin mutane a Afirka da Asiya
    Yadda cutar Typhiod ke barazana ga rayuwar miliyoyin mutane a Afirka da Asiya 06.07.2026 10m
    Shirin na Lafiya Jari ce zai a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan zazzaɓin Typhoid, cuta mai haɗari wadda ƙwayar cutar Salmonella Typhi ke haddasawa, inda ta kan yaɗu ta hanyar abinci ko ruwan da ya gurɓata.
  • Ƙaruwar masu fama da cutar sikila a Jamhuriyar Kamaru
    Ƙaruwar masu fama da cutar sikila a Jamhuriyar Kamaru 29.06.2026 10m
    A wannan makon shirin ya yi duba ne kan ƙaruwar masu fama da cutar sikila a jamhuriyyar Kamaru bayan fitar wani rahoto da ke cewa cikin shekara 1 kaɗai an tattara alƙaluman sabbin mutum dubu 6 da aka gano suna ɗauke da cutar. Wannan cuta mai alaƙa da nau’in jini, na daga cikin matakan yaƙi da ita shi ne tabbatar da gwaje-gwajen jini tun kafin aure don kaucewa haifar yara masu ɗauke da ita, ganin cewa hanya ɗaya tal ta samun masu cutar shi ne ta hanyar gado wato daga iyaye.

Popular in

The podcast also appears in the podcast charts of these countries.